Allon Wuta Mai Ƙōnāwa
Da sūnan Allah, madawwami, mafi girma. A gaskiya, zūkācen aminnai nā tōyēwa cikin wutar rabuwa: Inā ƙyalƙyalin hasken fuskarka, yā kai abun ƙaunar dūniyōyi?
Waɗanda suke kusanka, gā su cikin duhun rūdāni: Inā ƙyalƙyalin sāfiyar haɗuwa da kai, yā kai abun bēgen dūniyōyi?
Jikin zāɓāɓɓunka suna konce suna shēƙa bisa turɓuwa mai nīsa: Inā tēkun kasancēwarka, yā kai mai wadātar da dūniyōyi?
Gā hannuwa māsu rōƙo nā nufa wajen samāniyar alfarmarka da karāmarka: Inā ruwan alhērinka, yā kai da kake ƙāyatar da dūniyōyi?
Azzāluman kāfirai nā ɓullōwa daga kō’ina: Inā īkon alƙalamin dōkōkinka da bā a gōcēwa, yā kai mai nasara bisa dūniyōyi?
Ana jin karnuka nā habshi daga kō’ina: Inā zākin dājin ƙarfinka, yā kai mai hukunta dūniyōyi?
Ɗāri na suƙe ƴan adam gabāɗayansu: Inā gumin ƙaunarka, yā kai mai zāzafa duniyōyi?
Balā’i yā kai matuƙa: Inā alāmōmin tallafinka, yā kai mai cēton dūniyōyi?
Baƙin duhu yā lulluɓe yawancin al’ummmōmi: Inā hasken martabarka, yā kai mai ƙāwata dūniyōyi?
Ƙēyōyin mutāne sun yi gautsi dōmin ƙēta: Inā takubban fansarka, yā kai mai ragwargwaza dūniyōyi?
Sākarci yā kai matuƙa: Inā tūtōtin ɗaukakarka, yā kai maɗaukakin dūniyōyi?
Darūra tā māmāye wanda ya bayyana sūnanka: Inā murnar assubāhin bayyanarka, yā kai dāɗin dūniyōyi?
Rūɗāni yā māmāye duka al’ummōmin dōron ƙasa: Inā tūtōtin fara’arka, yā kai murnar dūniyōyi?
Kana ganin ana lulluɓe gabashin alāmōminka da habaicin sākarci: Inā yātsun īkonka, yā kai mamalakin dūniyōyi?
Ƙishirwa mai tsanani tana kāda duka ƴan adam: Inā gulbin karāmarka, yā kai arrahamānin dūniyōyi?
Haɗama tā mallaki duka ƴan adam: Inā wanda sū nē shaidar dangana, yā kai Ubangijin dūniyōyi?
Kana ganin wannan, wanda aka zālunta shī kaɗai cikin hijirarsa: Inā rundunōnin samāniyar hukuncinka, yā kai sarkin dūniyā?
An bar ni cikin ƙasa da bā tāwa ba: Inā tūtōcin amānarka, yā kai madōgarin dūniyōyi?
Mutuwa nā gabātar duka ƴan adam: Inā ambāliyar tēkun rāyuwarka, yā kai rāyuwar dūniyōyi?
Raɗe-raden nalīsa nā rātsa yawancin mutāne: Inā garwashin wutarka, yā kai fitilar dūniyōyi?
Dāɗin annashuwa nā rāzana yawancin mutāne: Inā tāhirin jijjibi, yā kai abun bēgen dūniyōyi?
Kana ganin zālunci yana murƙushe wannan bāwan Allah a ƙasar sīriya: Inā ƙyalƙyalin haskenka da ya fāra kunnōwa, yā kai hasken dūniyōyi?
Kana ganī an hanā ni magana: Daga inā āyōyinka zā su ɓullo, yā kai sūdar dūniyōyi?
Shirmē da tunānin wōfi sun dabaibaye yawancin mutāne: Inā māsu fasara gaskiyarka, yā kai hakīkar dūniyōyi?
Bahā nā lumēwa cikin tēkun azāba: Inā al’arshin tsīrarka, yā kai mai kubtar da dūniyōyi?
Kana ganin sāfiyar kalmarka tā ɓace cikin duhun halitta: Inā rānar samāniyar alfarmarka, yā kai jāgōran dūniyōyi?
Fitilōlin gaskiya da tāhir, biyyaya da ɗiyauci sun mutu: Inā alāmun fushinka mai rāmāwa, yā kai injin dūniyōyi?
Bābu kō mutun guda da ya kāmāwa Manzonka, kō ya yi nazari bisa matsalōlin da ya gabātar bisa hanyar ƙaunarka: Gā shi alƙalamīna ya būshe, yā kai masōyin dūniyōyi?
Iskar ƙaddara ta karya rassun iccen aljanna, sun zuɓe a ƙasa: Inā tūtōtin āgajinka, yā kai mai kāre dūniyōyi?
Ƙūrar ba’a tā ɓōye wannan fuskā: Inā bazarar jinƙanka, yā kai arrahamānun dūniyōyi?
Al’ummar munāfikai nā ɓāta rigar tsabta: Inā taguwar tsarkakarka, yā kai mai suturar da dūniyōyi?
Ayyukan mutāne nā dākatar da tēkun alfarma: Inā igiyōyin karāmarka, yā kai abun bēgen dūniyōyi?
Zāluncin maƙiyanka, sun kulle ƙōfar dake kai garēka: Inā mabūɗin alhērinka, yā kai mai būda ƙōfōfin dūniyōyi?
Iskā mai ɗauke da gubar adāwa nā ƙēkāshe ganyāye: Inā yayyafin gizāgizan karāmarka, yā kai mayalwacin dūniyōyi?
Ƙūrar zunubi, nā duhuntar da sararin samāniya: Inā bazarar gāfararka, yā kai mai gāfartāwa dūniyōyi?
Wannan matāshi, yana nan shī kaɗai cikin hamāda: Inā rūwan alfarmarka ta samāniya, yā kai mai baiwā dūniyōyi?
Yā alƙalamin ƙōli, mun ji kiranka mai dāɗi cikin daula madawwamiya: ka shūrāri abun da harshen girmā yake faɗi, yā kai ma shā wuyan dūnoyōyi?
Idan bābu ɗāri, yāyā gumin kalmarka zai bayyana, yā kai mai fasarar da dūniyōyi?
Idan bābu balā’i, yāyā hasken rānar jūriyarka zai ganu, yā kai hasken dūniyōyi?
Kada ka yi jājē sabōda maƙētatā. An halittō ka don a ƙuntatā maka, kuma ka yi jūriya, yā kai mahaƙurcin dūniyōyi?
Bayyanarka cikin māsu adāwa a jiririn alƙawalinka, abun nishāɗi nē, kuma jūyāwa wajen Allah abun jin dāɗī nē, yā kai ƙaunar dūniyōyi!
Kā kafa tūtar ƴanci bisa ƙōlōluwar birji, kuma kā ɓullo tēkun karāma, yā zumūɗin dūniyōyi!
Kaɗaitakarka nā gwada ƙyalƙyalin rānar ɗayantaka, kuma hijirarka nā ƙāyatar da ƙasar kaiɗaita. Ka yi jūriya, yā kai bāƙon hauren dūniyōyi!
Mun maida ƙasƙantā tamkar rigar ɗaukakarka, azāba adon gidan ibādarka, yā kai abun kirārin dūniyōyi!
Kana ganin zukāce cike da ƙiyayya, tō ka yi haƙuri, yā kai da kake ɓōyē zunubban dūniyōyi!
Idan an zāro maka takōbi, kada ka jā da bāya: idan an halbō maka kibiya, ka gaggauto ka nufē ta, yā kai sadaukin dūniyōyi!
Kai zā ka zubda hawāye, kō nī zan zubda? Yā cancanta in yi kūka gaban māsu kārē ka dake ƙalīlan, yā kai tūshen kōke-kōken dūniyōyi!
Hakīka, ina jin kiranka, yā kai mafi ɗaukaka, abun ƙauna! Yanzu zāfin azāba da wutar kalmarka mai armashi nā haskaka fuskar Bahā. Sai ya gabāci wurin sadaukarwa cikin amāna, yana son kaiwa ga abun da kake sō, yā kai mai shirya dūniyōyi!
Ya kai Ali Akbar, ka gōdēwa Ubangijinka dōmin wannan allo. Kana iya jin ƙamshin tawālina, kuma ka gāne da rūdānin da muka gabāta bisa hanyar Ubangiji Allah subahānahu wa ta āla, wanda kōwa yake wā ibāda. Bāwan da ya jā, kuma ya yi nazari bisa wannan āyā, wuta nā kunnuwā cikin jījīyar jininsa, da zā ta māmāye dūniyōyi.