Prayers & Meditations
Hausa ·
Idan an zāɓi yin wannan salla, a bāyan an yi arwalla, a tāshi, a jūya gabā gabas maso arēwa, a dūbi dāma da hauni, tamkar mai nēman rahamar Ubangiji, ar-rahamane, mai jinƙai, kuma a cē :
Yā kai wanda kai nē Ubangijin duka sunāyē, kuma mahaliccin sammai ! dōmin darajar waɗanda sū nē asubāhin zātinka mai girma, ma fi ɗaukaka, da ya wuce a gāne Shi, ina rōƙon ka sā sallāta, ta zamana tamkar wutar da zā ta ƙōnē yānar dake hanā ni ganin kyāwonka, kuma ta haske hanyāta zuwa tēkun kusantarka.
A ɗaga hannuwa wajen Ubangiji, yabo da ɗaukaka su tabbata a garēshe, a cē:
Yā kai buƙātar dūniya, gātan duka al’umma, kana gani nā jūwa huskāta wajenka, cikin wātsi da duka wata dōgara ga kōwa in bā kai ba, kuma riƙe da igiyarka wadda mōtsinta nē yake mōtsa halitta gabāɗayanta. Yā kai Ubangijina, nī bāwanka nē, kuma ɗan bāwanka. Kana gani nā shirya cika ƙudurarka, kuma da abun da kake sō. Bā nā son kōmai, sai abunda kake sō.
Ta hanyar tēkun rahamarka da rānar alfurmarka, ina rōƙon ka ɗōrāwa bāwanka abun da kake sō, da ya dāce a garēka. Nā rantse da īkonka da ya wuce kwatamci da kirāri, duka abun da ka bayyana, shīnē gūrin zūciyāta da abun ƙaunar rūhūna.
Yā Allah Ubangijina, kada ka dūbi nufīna kō aikīna, amma ka dūbi īkonka wanda ya lulluɓe sama da ƙasa. Yā kai Ugangijin duka al’umma, da sūnanka mafi girma, bā na buƙātar kōmi, in bā abun da kake buƙāta ba, kuma bā nā son kōmi in ba abun da kake sō ba.
A durƙusa, kuma gōshi bisa ƙasa a cē :
Ɗaukakarka tā wuce duk wani kwatamci wanda bā nāka ba, kuma tā wuce fahimtar kōwa in bā tāka ba.
A tāshi, a cē :
Yā Ubangijina, ka maida sallāta marmaron ruwa garai da zā ya rāyar da ni har abada, kuma sallar nan, ta sā in ambacē ka cikin kōwace dūniyarka.
A tāshi, kuma a ɗaga hannuwa cikin rōƙo, a cē:
Yā kai da kake zāzafa zūkāce da rūhunnai idan sun nīsanta da kai, kuma da kake haske dūniya gabāɗayanta da hasken sōyayyarka! Da sūnanka mai sanyaya duka ran halitta, ina rōƙon kada ka hanā mani duka abun da yake nāka, yā kai mai īkon duka ƴan adam! Yā Ubangijina, kanā ganin wannan bāƙon yana gaugautāwa wajen mabartarsa mafi ɗaukaka, ƙalƙashin runfar martabarka, gaban bangon rahamarka, wannan mazunubanci da yake nēman tēkun gāfararka, wannan ƙasƙantacce da yake zuwa nufa fādar ɗaukakarka, wannan miskīni da yake nēman arzikinka.
Kai kake umurta abun da kake sō! Nā shaida cēwa, yabo yā cancanca ga duka ƙudurarka da abun da ka aikata, kuma cikkaken ƴinci yā tabbata ga dokokinka.
A ɗaga hannuwa, a jā “Allah’u’Abha” sau uku. A dūƙa gaban Ubangiji (albarka da yabo su tabbata a garēshi), a ɗōra hannuwa bisa gwiwōwi, a cē :
Yā Allāna, kana ganin yanda dukāna nake cike da buƙātar yabonka, da kuzārin kiran sūnanka, kuma da yaba ka; kana ganin yadda rūhuna yake fadaƙar da abun da harshen dōkarka ya ƙayyada cikin daular kalmarka, kuma bisa samāniyar iliminka. Yā Ubangijina, cikin wannan hālin da raina yake, ina ƙaunar tambayarka duka abun dake nāka nē, tunda nī maskīni nē, ina ɗaukaka alhērinka da arzikinka, tunda nī talakka nē, ina tabbatar da īkonka da ƙarfinka.
A mīƙe, kuma a ɗaga hannuwa sau biyu, a rōƙi cēwa:
Bābu wani Allah sai kai, mai ƙudura, mai yalwā maras iyāka. Bābu wani Allah sai kai, ma’umurcin farko da na ƙarshe. Yā Ubangiji Allāna, afuwarka tā bāni kuzāri, kuma rahamarka tā ƙarfafa ni; kiranka yā falkar da ni, alfurmarka tā ɗaga nī zuwa garēka. Idan bā haka ba, ta yāya zā ni tarki tsayāwa ƙōfar fādarka, kō kuma in ɗaga fuskāta wajen hasken dake ƙyalƙyali daga samāniyar ƙudurarka ?
Yā Ubangijina, kana ganin wannan miskīni yana ƙyarƙyara ƙōfar alfurmarka, wannan rūhu nā nēman ƙōramar rāyuwar har abada, daga cikin hannun yalwarka.
Yā kai Ubangijin duka sunaye, īko yana garēka kōwane lōkaci, nī kuma haƙuri da ladabi ga ƙudurarka, sū nē nāwa, yā mahaliccin sammai !
A ɗaga hannuwa sau uku, a cē:
Allah shīnē mafi girma!
A ɗurƙusa goshi a ƙasa, a cē :
Ɗaukakarka tā wuce matsayin da yabon māsu kusantaka da kai, ya isa samāniyar fadarka, kō tsuntsāyen zūkācen masōyanka su kai ƙōfarka.
Nā shaida cēwa, tsarkakarka tā wuce kōwane laƙani da kōwane sūna. Babu wani Allah sai kai, mai mulki, maɗaukakin sarki.
A zauna a cē :
Kamar duk halittu, malā’ikun samāniya, mazaunan aljannar ƙōli, kuma sama da su, mazaunan sararin samāniyar ɗaukaka, da harshen martaba shi da kansa, nā shaida cēwa, kai nē Allah, bā ka da abōkin tārayya, kuma wanda ka manzonta shīnē, bōyeyyen gaibu, shīnē alāma mai daraja. Ta garēshi aka haɗa baƙaƙe k-a-s-a-n-c-e (kasance), kuma aka haɗā su, aka ɗaure su.
Nā shaida cēwa, sūnansa nē alƙalamin ƙudura da irāda ya rubuta, kuma aka ambata cikin litattafan Allah Ubangijin karagun sama da ƙasa.
A tāshi a cē :
Yā kai Ubangijin duk halitta, kuma mamallakin duka abūbūwan da ake gani kō dake ɓōye, kana ganin hawāyēna, kana jin nīshīna, kana jin kūkāna, gungunīna da takaicin dake zūciyāta. Don girmanka, laifuffukāna suna hana ni kusanta da kai, kuma zunubaina, nā nīsantā ni da tsarkakarka.
Yā Ubangijina, ƙaunarka nā arzitar da ni, rabuwa da kai nā hallakā ni, kuma nīsanta da kai, nā tōya ni rumus. Da sūnan sāwunka cikin hamāda, ta wannan kalmōmi «gā ni, gā ni !» da gātāyanka suke faɗa cikin sarari, da sūnan numfāshin bayyanarka, da iskar sāhiyar wahayinka, ina rōƙon ka yarda, in kalli kyāwonka, kuma in bi duka abun dake cikin kitābinka.
A jā Allah’u’Abha sau uku, a ɗūka, hannuwa bisa gwīwōwi a cē :
Yabo ya tabbata a garēka yā Allāna! kana taimako nā da tunāni da kai, kuma da yabāwa da kai. Kana sanarshe ni da wanda shīnē assubāhin āyōyinka. Kana sā ni dūƙāwa gaban īkonka, durƙusāwa gabanka, kuma da yarda da abunda harshen girmā ya ayyana.
A tāshi, a cē :
Yā Allah Ubangijina, nauyin zunubaina yā sā na yi dōro, kuma sakacīna yā hallakā ni. Idan na yi nazari bisa laifufukāna da alhērinka, zūciyāta sai ta kātse, jikīna ya yi sanyi. Yā kai abun shāwar duka dūniya, dōmin kyāwonka, sai na ji kunyar ɗaga fuskāta wajenka, kuma na ji kunyar ɗaga hannuwāna, dōmin rōƙo wajen samāniyar alhērinka.
Yā Allāna, kana ganin yanda hawāyēna suke hana mani ambatar ka da yaba iyāwarka, yā kai Ubangijin karagun sama da ƙasa! Don sabōda alāmun īkonka, kuma da gaibun daularka, ina rōƙon, ka dūbi masōyanka da idon alfurmarka, yā kai sarkin abūbūwan da ake gani da na ɓōye.
A jā Allah’u’Abha sau uku, a durƙusa, gōshi a ƙasa a cē :
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allah! Kana bayyana muna abun da yake kusantar mu da kai, kuma kana bā mu duka alhērin dake cikin litattafai da kitābōbinka.
Yā Ubangijinmu, muna rōƙon ka kāre mu da rundunar tunāninmu na wōfi, da ra’āyōyinmu na shirme. A gaskiya, kai nē mai ƙudura, masanin kōmi.
A tāshi tsaye a ce:
Yā Allāna, nā shaida abūbūwan da gātāyanka suka shaida, kuma nā faɗakar da abun da mazaunan aljanna, da waɗanda suke kēwaye da karagar fādarka, suka faɗakar. Daulōlin ƙasa da na sama duka nāka ne, yā Ubangijin dūniyōyi.
Yā Allah Ubangijina, kar ka kasance nēsa da ni, sabōda matsalōli sun māmāye ni. Yā Allah Ubangijina, kar ka bar ni in cēci kaina da kaina, alhāli ƙiyayya mai tsanani tā hayyacē ni. Ka ƙōsar da ni da tātāccen nōnon karāmarka, sabōda ƙishurwa tā kāma ni matuƙa. A ƙalƙashin fufuken rahamarka, ka kāre ni sabōda maƙiyāna sun haɗu sun zāburo mani gabāɗayansu. Tsare ni kusan gadon mulkinka, gaban alāmu māsu nūna dawwamarka har abada, sabōda ƙarfīna yā ƙāre. Da luddan ruwan murna da hannun rahamarka ya mīko, ka haƙurar da ni, sabōda baƙin ciki mai nauyi yā tsananta mani. Ka rufe ni da rīga mai zubin cikakken īkonka, sabōda talauci ya yāce ni gabāɗayāna. Ka yarda in hūta cikin saurāren tāwan kūkan kurciyar samāniyarka, sabōda baƙar darūra tā rufe ni.
A gaban gadon ɗayantakarka da hasken kyaukyawar huskarka, ka sā in tsaya, sabōda tsōro da karkarwa sun hallaka ni. A cikin kōgin rangwamenka nike sō ka zundumā ni, sabōda yawan zunubbaina sun ɓatar da ni gabāɗayāna.
Wannan āyā, ana jan ta a ƙabarin Baha’u’llah, kō na Bab (tsīra da aminci su tabbata a garēsu). Wanda yake sō, yana iya karantā ta, rānēkun haifuwarsu.
Yabo dake dangance da zamantakēwarka mai martaba, kuma da mahibbar da ta haskō daga ƙyalƙyalin kyāwonka, su tabbata a garēka, yā kai da kai nē alāmar girma, da kai nē sarkin dawwama har abada, kuma da kai nē Ubangijin duk abūbūwan dake ƙasa da sammai !
Nā shaida cēwa, ta garēka nē, mulkin Ubangiji Allah, martabarsa da girmansa, suka bayyana, taurārun sāfiyar kyaukyāwar dauri, suka baza haskensu da bā ya shūɗēwa, cikin samāniyar kudurinka, kuma kyāwon wanda bā ya ganuwa, ya haske jiririn halitta.
Nā shaida kuma da cēwa, daga rubūtun alƙalaminka guda, sai umarninka « kasance » ya aikata, ɓōyeyyen gaibun Ubangiji Allah ya bayyana, ka rāya duka halittu, kuma duka wahāyi ya sauko.
Nā shaida cēwa, ta kyāwonka nē, kyāwon wanda shīnē abun yabo ya bayyana, kuma ta fuskarka cē, fuskar wanda shīnē abun ƙauna ta fitō hīli, kuma da kalmā guda, ka ƙayyada matsayin duk halitta, ka ɗaukaka wanɗanda suka yi īmāni har zuwa ƙōli, kuma ka jēfa kāfirai cikin rāmi mai zurfi.
Nā shaida cēwa, wanda ya amince da kai, yā amince da Allah Ubangiji Subahānahu wa ta āla, kuma wanda ya kai garēka, yā kai ga Ubangiji Allah. Albarka ta tabbata ga wanda ya yarda da kai kuma da alāmunka, ya gwada tawāli gaban martabarka, kuma ya sāmu sāduwa da kai, ya cinma bukātunka, ya jāƙuɗo kusanka, kuma ya durƙusa gaban karagarka.
Hallaka ta tabatta : ga wanda ya ɗauki zunubi garēka, ya yi wātsi da kai, ya yi jīfa da alāmunka, ya ƙi yarda da martabarka, kuma ya tāshi ya kai maka hari, ya gwada girman kai a gabanka, ya ƙi karɓar shaidōdinka, ya kēɓēwa dōkōkinka, ya yi adāwa da ikonka, ya shiga cikin kāfiran nan da sūnāyansu suke rubūce bisa tsarkakkun allunan ƙudurarka.
Daga dāmar rahamarka da alhērinka, ka sauko mani, yā Allah Ubangijina, abun ƙaunāta, tsarkakakkar bazarar alhērinka, dōmin ta ƙēɓē ni da nī kaina, kuma da dūniya, sabōda ta jāgōrancē ni wajen dandalin kusantarka da kaiwa garēka. Kana da īkon aikata abun da ka ga dāma, hakīka, kai nē bisa ga kōmi da kōwa.
Ambatar Ubangiji Allah, da yabonsa, ɗaukakarsa da girmansa su tabatta a garēka, yā kai wanda kai nē kyāwonsa ! Nā shaida da cēwa, bābu idon halittar da ya kalli wanda aka zālunta kamar kai. Duk rāyuwarka, an zunduma ka cikin tēkun rūdāni. A wani lōkaci, an ɗaure ka da sarƙa da mari, a wani lōkaci kuma, maƙiyyanka sun zāre maka takubbansu. Amma, duk da haka, kā gayyaci mutāne, da su bi umarnin da wanda shīnē al’alīmu, mai hikima maras iyāka, ya sauko a garēka.
Ina rokon Ubangiji, da ya karɓi rūhūna, tamkar tōshi, dōmin wahalōlin da ka gabāta, kuma ya amshi raina sabōda adāwar da aka maka. Ina roƙon ka, don darajarka da waɗanda fuskarsu ta sāmu ƙyalƙyalin hasken fuskarka, waɗanda don matuƙar ƙaunarka, suka karɓi duk abūbūwan da ka umarcē su da yi, ka kēta lābilen da ya raba ka da halittarka, kuma ka bā ni alhērin dūniya da na lāhira. A gaskiya, kai nē al’azīzu, kai nē al’alīyu, mafi ɗaukaka, mai gāfartāwa har kullun, mai jin-ƙai.
Yā Ubangiji Allāna, ka albarkatar da itāciyar Ubangiji, da ganyenta, da rassunta, da tsironta, da karanta, da ƴāƴanta, har iyākar tsawon sūnāyenka māsu martaba, da laƙanunka mafi ɗaukaka. Ka kāre su, da harin maƙiya, da rundunōnin azzālumai. A gaskiya, kai nē al’azīzu, al ƙādiru. Yā Allāna, ka albarkatar da bāyinka maza da māta, da suka isō garēka. A gaskiya, kai nē mai rahama, wanda alfarmarsa bā ta da iyāka.
Bābu wani Allah illa kai, mai gāfartāwa a kullun, mayalwaci.
Ya jalla, Ubangiji Allāna ! Ina maka gōdiya da ka sā a cikin yardarka, na bāda gaskiya da tabbatarka, ka kubtar da ni daga cikin maƙiyanka, ka būɗe idānūna har na gāne da mummūnan abūbūwan da suke aikatāwa, ka kēɓē ni da duk wata rātaya da su, ka sā na maida duk al’amurrāna zuwa ga alhurmarka da karāmarka.
Ina maka gōdiya, yā Ubangijina, da ka saukar mani daga gizāgizan yardarka, abūbūwan da suka kāre ni da habaicin kāfirai, kuma da ba’ar la’anannu, ka sā na kafa zūciyāta zuwa tunāninka, ka sā na yi nēsa da waɗanda suka ƙi gānēwa da hasken huskarka.
Ina kuma gōdiya, da ka bā ni dāmar in kasance tsayayye cikin ƙaunarka, in yi yabonka, in ɗaukaka sūnanka. Ina maka gōdiya, da ka ƙōsar da ni da ruwan rahama, wanda darajarsu, ta haye duk wasu abūbūwan da suka bayyana, kō suke ɓōye.
Kai nē Jalla, mafi ɗaukaka, mai cikakkar ƙauna.
Idan an zāɓi yin wannan salla, a bāyan an yi arwalla, sai a jā wannan āyā da sāfe, da rāna, kuma da dare kōwace rāna.
Ana tsaye, a jūya fuska wajen ƙibla, a cē :
Allah yā tabbata cēwa, bābu wani Allah sai Shi. Daulōlin wahayi da halittu duka nāsa nē. A gaskiya, yā bayyana wanda shīnē asubāhin wahayi, wanda ya zanta bisa sinaï, wanda ta garēshi maɗaukakin haske ya haska, wanda ta garēshi itāciya mai martaba wanda bāyanta bābu wata hanya, kuma wanda ta garēsta aka yi wannan kira zuwa ga duk waɗanda suke sama da ƙasa cēwa: «Gā wanda shīnē mai kōwa mai kōmi yā iso. Ƙasa da sama, ɗaukaka da ƙudra mallakar Allah nē, Ubangijin duka ƴan adam, kuma mai mallakar mulkin sama da na ƙasa. »
A dūƙa, hannuwa bisa gwiwōwi, a cē:
Kā fi ƙarfin yabōna da yabon kōwa, kā fi ƙarfin kwatamcina kō na duk mazaunan sama da ƙasa!
Kuma a tāshi tsaye, hannuwa a būɗe wajan fuskā, a cē:
Yā Allāna, kada ka yi wātsi da wanda yake mīƙa hannuwan rōƙō a garēka, sarƙafe ga rīgar rahamarka da karāmarka, yā kai mafi rahama cikin māsu aikata rahama.
A zauna a cē :
Nā tabbata cēwa, da kai kaɗai kake, kuma bā ka da abōkin tārayya, kai nē Allah, kuma bābu wani Allah sai kai.
A gaskiya, kā bayyana addīninka, kā cika alkawalinka, kuma kā būɗa ƙōfar alfurmarka warai, ga duk waɗanda sukē sama da ƙasa. Albarka da sallama, tsīra da ɗaukaka, su tabbata ga masōyanka, waɗanda sauye-sauye da harakōkin dūniya, ba su hana su ba jūyāwa wajenka, kuma waɗanda suka yi wātsi da duk abūbūwansu, dōmin su sāmu abunda kē tāre da kai.
A gaskiya, kai nē mai jinƙai har abada, mai yalwa.
Idan an fi sō, ana iya karanta waɗannan gajērun āyōyi, kambacin waɗanda kē bāya; ana tsaye a cē:
Allah yā tabbata cēwa, bābu wani Allah sai Shi, mai cēto cikin matsala, mabuwāyi.
Ana zaune, a cē :
Nā tabbata da kai kaɗai kake, bā ka da abōkin tārayya, kai nē Allah, kuma bābu wani Ubangiji sai kai.
Yabo ya tabbata a garēka, yā Allāna! Kai nē wanda daga būɗa bāki, sai duka dūniya ta yi gilgiza, wanda daga kurta alƙalaminka, ka rarraba bāyunka. Nā shaida yā Allāna, da cēwa, a wannan wahayi, kalmarka guda ɗaya tā sā duk halitta tā zama mai hallaka, kuma da wata kalmar, duk wanɗanda ka zāɓā, suka rāyu da sābuwar rāyuwa, dōmin alfurmarka da karāmarka. Sabōda haka, nike maka gōdiya da yabo, don darajar duk waɗanda kake ƙauna, waɗanda ka sāke rāyāwa da ruwa māsu rāyarwa, da suka ɓullo daga marmaron yardarka.
Tunda yake, kā rāyar da su a cikin alhērinka mai girma, yā Allāna, ka sā hankalinsu ya kōma zuwa wajen umurninka. Da yake kā yarde musu, shiga cikin ɗākin addīninka, ka yarde musu a cikin alfurmarka, kada kōmi, ya riƙe su nēsa da kai. Ka būɗe mā zukācensu yā Allāna, ƙōfōfin saninka, don su gāne da kai nē wanda ya fi a gāne shi, wanda duk halitta ba ta isa ta farga da iyākacinsa ba, wanda yake yā wuce inda, kōmin ƙōƙarin bāyinka, su fahimta da yanda kake ciki, kuma ka wanke zukācensu, dōmin kada su kula da waɗannen maƙaryata, māsu yawan sūrūtu da suke ƙariyar batu da sūnanka.
Yā Ubangijina, ka bā bāyin nan nāka, hamzarin da zā su sarkafa a addīninka da kuzāri ta yanda har abada, bā zā su kula ba da habaicin wanɗanda ba su sā kōmi gaba ba, in bā abun dūniya ba, masu aikata abūbūwan da ka hana a cikin litattafanka da kitābanka. Kā san yā Allāna, ina jin kūkan kūrāyen da suke bayyana da kamannin bāyinka. Ka kāre masōyanka da sharrinsu, kuma ka yarda su riƙe abin da ka bayyana cikin wanan wahayi nāka wanda cikin saninka, ka ƙayyada cēwa, bā shi abōkin tārayya.
Ka isar musu, yā Allāna, da abun cin mōriya, ka haske su da hasken saninka don su fahimta da kai nē sama ga kōmi, kuma su shaida da ɗaukakarka a bisa halittarka da nasararka ga waɗanda suke sama da na ƙasa. Ka na da īkon aikata kōmi, yanda ka ga dāma. Bābu wani Allah in ba kai ba. Kai nē jalla, wanda duk tāliki yake rōƙon taimakonka.
Yabo ya tabbata a garēka, yā kai Ubangijin tālikai.
Yā Ubangiji Allah maɗaukakin Sarki ! Ina rōƙon ka da sūnanka wanda ta garēshi ka ɗōra wanda shīnē kyāwonka, bisa kujērar īkon addīninka, sūnanka wanda da shīnē, kake sauyā kōmi, kuma kake haɗa kōmi, sūnanka dake hukunta kōmi, kake sallamar kōmi, kake kāre kōmi.
Ina rōƙon ka kāre baiwarka wadda ta nēmi ɓūya garēka, kuma take nēman kāriyar wanda garēshi ka bayyana. Wannan baiwar tā mīƙa duka gūrinta da amincinta a garēka. Bā ta da lāfiya yā Allāna! Amma tā shiga ƙalƙashin inuwar iccen warkarwarka. Tā furgita, sai ta tsēro cikin birnin taimakonka, cūta tā kāda ta, sai ta nēmi ɗugon ruwan rangwamenka, tā tsōrata, sai ta zābura don ta iske ƙōramar kwanciyar hankalinka, tā ɗau zunubi, sai ta maida fuskarta wajen dakalin gāfararka. Ka rufēta a cikin īkonka, da mayāfin warkarwarka da alhurmarka, yā Allāna, abun ƙaunāta! Ka kōri ƙishirwarta da kāriyar rahamarka da ni’imarka. Ka kāre mata duk wata azāba, matsala kō cūta, kuma da duk wani abun da yake la’ananne a ganinka.
A gaskiya, kai nē wanda ka fi ɗaukaka bisa ga kōmi in ba kai da kanka ba. Hakīka, kai nē mai warkarwa, wanda ya isa ga kōmi, mai kārēwa, mai jin-ƙai har abada, mai rahama.
Dukan yabo ya tabbata a garēka yā Ubangiji Allāna ! Ina rōƙon ka, da sūnanka mai martaba da aka tsare cikin kurkukun birnin Akka, wanda ya fāɗā hannun maƙiyansa, kuma la’anannu suka zāre masa takubbansu, ka bā ni ƙarfin da zan zama tsayayye cikin addininsa, kuma in jūya kallōna wajensa, ta yanda bā wanda ya isa ya karkatar da ni.
Nā shaida yā Ubangijina cēwa, yā bāyar da ransa bisa hanyarka, kuma don tsananin ƙaunarka, yā gwammace da wahala. Bābu cin mutuncin da ba a masa ba, don yā bayyanar da mulkinka zuwa ga bāyunka, kuma yā ɗaukaka kalmarka gaban halittarka. Kō da yake, matsalōli suna ƙāra cī gaba, kuma darūrar da ka zubo masa tā māmāye shi ta kō’ina, sai ya ƙarfafa cikin tunāninka, har ya zamanto duk yawan waɗanda suka wātsar da alāmunka, kuma su ka ƙi bāda gaskiya a garēka, sun daina bā shi tsōro.
Ina rōƙon ka, yā Ubangijina, a bisa darajarsa da duk abunda yake nāsa nē, ka sā ƙaunāta ta tabbata a garēshi, kamar yanda ƙaunarsa ta tabbata a garēka.
Nā shaida da cēwa, ƙaunarsa ƙaunarka cē, bayyanarsa bayyanarka ce, haskensa haskenka nē, kuma addininsa addininka ne.
Kada ka hana mani yā Ubangijina, abun da ka mallaka, kada ka dāmu don nā mance abun da kake sō a rānēkunka. Hakīka, kai nē mabuwāyi, maɗaukakin sarki, jalla mafi basīra.
Yabo ya tabbata a garēka yā Ubangiji Allāna. Ina rōƙon ka, don darajar wannan bayyana, da ta maida duhu haske, kuma da garēta a ka gina masallacin jama’a, da garēta kuma aka sauko rubutaccen allo, a ka shinfida ɓoyayyan kundi, ina rōƙon ka sauko mana, ni da abōkan zamāna, abun da zai sā mu hira wajen samāniyar ɗaukakarka, kuma abun da zai tsarkakar da mu da dauɗar shakka da ta hana waɗanda ba su amince ba, shiga cikin zauren ɗayantakarka. Yā Ubangijina, gā ni, nī nē wanda ya sarƙafu ga igiyar alfurmarka, kuma ya rātayu ga zanen rahama da alhērinka. Ka zubo mana ni da duk waɗanda nike ƙauna, albarkan nan da ka wārewa zāɓaɓɓun bāyunka.
Yā Ubangijina, ga rānaikun da ka umurci bāyunka da ɗaukan azumi. Albarka ta tabatta ga wanda ya ɗauki ƙishurwa, kawai sabōda ƙaunarka, kuma cikin wātsi da kōmi in ba kai ba. Ka taimakē ni kuma ka tamaike su, yā Ubangijina, don mu bi umurninka, kuma mu tsaida dōkōkinka.
A gaskiya ka nā da īkon yin abin da ka ga dāma. Bābu wani Allah illā kai, mafi sani da basīra. Dukan yabo ya tabbata ga Allah Ubangijin duka dūniya.
Yabo da ɗaukaka su tabbata a garēka yā Allāna. Ina rōƙon ka, don darajar shaidar māsu ƙaunarka, da hawāyen waɗanda suke tsananin buƙātar ganin ka, kar ka hana mani rahamarka a wannan babbar rānā tāka, kuma kar ka hana ni jin kūkan tantabarar nan mai wāka ɗayantakarka a gaban hasken huskarka.
Kana gani nā cikin tsananin talauci yā Ubangijina ! Gā shi nā sarkafa ga sūnanka mai mallaƙar kōmi. Nā san kat, da ina hallaka, sai gāshi nā sarkahu ga sūnanka wanda ya fi gaban hallaka. Don haka nē, nike rōƙon ka, don zātinka mai martaba, maɗaukaki, kar ka bar ni in fāɗa cikin miyāgun ayyuka. Ka riƙe hannūna cikin hannunka mai ƙarfi, ka zāgo ni daga cikin zurfin ra’ayīna karkatacce, ka hudda mani duk wani tunānīna na wōfi, kuma ka tsarkake ni da duk abun da ka yi wātsi da shi. Ka bā ni ƴancin jūyāwā gabāɗayāna wajenka, in amince da kai, in yi gudu wajenka nēman ɓūya, kuma in zābura zuwa gaban huskarka. Kai nē, hakīka, wanda kake aikata abun da kake sō don girman īkonka, kuma cikin girman īkonka, kuma haka cikin girman mulkinka kake umurtar abin da ka ga dāma. Bā wanda ya iya tsayāwa gaban ƙaddararka, bābu wanda zai iya kēwaye nufinka. Gaskiya, kai nē ƙadiran, maɗaukaki mayalwaci.
Wannan salla ta zanā’ida, ana yin ta zuwa ga mariganyi baha’i mai shēkaru gōma sha biyar (15) a ƙalla. Wannan salla ita ƙadai cē ake iya yi a jam’i. Baha’i guda yake karantā ta gaban sauran mutāne da suke sahu a tsaye. Bā dōle ba nē, su jūya sahunsu wajen ƙibla.
Yā Allāna, gā bāwanka , ɗan bāwanka, da ya bāda gaskiya a garēka, kuma ya yarda da alāmōminka, yā jūya fuskarshi wajenka, bai sarƙafa da kōmi ba, in bā kai ba.
A gaskiya, kai nē mafi rahama cikin māsu rahama. Ka karɓē shi cikin samāniyar alhērinka da tēkun alfurmarka, yā kai mai gafartāwa ƴan adam, kuma mai ɓōye laifunsu! Ka yi masa marhaba cikin dandalin rahamarka mafi kwatamci, da kē nan kāfin halittar sama da ƙasa.
Mai karanta wannan salla, ya jā ‘’Allah’u’Abha’’ sau shidda (6), kuma ya jā kōwace āyā mai zuwa, sau gōma shā tara (19).
Allah’u’Abha (sau1)
A gaskiya, mū duka muna ƙaunar Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna durƙusāwa gaban Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna rōƙon Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna yabon Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna gōdiya ga Allah (sau 19)
Allah’u’Abha (sau 1)
A gaskiya, mū duka muna bin umarnin Allah (sau 19)
Yā Ubangiji, nā jūya huskāta wajen fādar ɗayantakarka, kuma nā nutsa kaina cikin tēkun rahamarka. Yā Ubangiji, ka wāye idānuwāna cikin wannan duhun, don tsinkāyen haskenka mai cikakken haskēwa, ka mayar da ni maji dāɗi a wannan zāmani mai abun al’ajabi ta wajen ɗanɗanon ƙaunarka.
Yā Ubangijina, ka sā in ji kiranka, ka kuma būɗe mani ƙōfōfin arshinka, dōmin in ga annurin ɗaukakarka, ta yanda zā ta huzgē ni zuwa wajenka.
Lalle, kai nē mai bayyanarwa, karīmin, mai rahama, mai yāfēwa.
Dukan yabo yā tabbata a garēka, yā Allah Ubangijina ; kai da kake tūshen girma da ɗaukaka, sarauta da mulki, natsuwa da alhēri, mai ban tsōro da īko. Ga wanda ka ga dāma, ka kan jāwo shi, kusa da mahīhīcin tēkunka mai girma. A kan wanda ka nufa, ka kan sanarshē shi da sūnanka na fil azal. Ga duka waɗanda kē sama da ƙasa, bā wanda zai iya tsayāwa ga nufinka mai girma. Tun fil azal, kā yi mulkin halittarka, kuma zā ka ci gaba da mallaƙar abin da ka hālittō da īkonka. Bā wani Ubangiji sai kai, mafi girma, mafi ɗaukaka, mafi īko da basīra.
Ka haskaka huskōkin bāyinka, dōmin su gan ka, ka wanke zukātansu, dōmin su jūya zuwa sāmun ni’imarka, kuma su bāda gaskiya ga wanda ya bayyana asīranka da babbar alfurmarka.
Bā shakka, kai nē Ubangijin duka dūniya. Bā wani Allah sai kai, mai nasara, mai mallaƙar kōmi.
Martaba ta tabbata ga sūnanka, yā Ubangiji Allāna! Kai nē wanda kōmi da kōwa yake bautāma, amma bā ka bautāwa kōwa, kai nē mamallakin kōwa da kōmi, amma bābu mai mallakarka. Kai nē masanin kōmi da kōwa, amma kā fi ƙarfin a san kōmi nāka.
Da ka sō mutane su san ka, sai da kalmarka guka ɗaya, ka rāya dūniya, kuma ka halicci duk abun dake sama da ƙasa. Bābu wani Allah sai kai, mahalicci, mai rāyāwa, maɗaukaki mabuwāyi.
Ina rōƙon ka, da wannan kalma da kā sauko daga irādarka, ka bā ni izinin shan ruwan nan rāyayyu, da ka rāya zukācen zāɓɓaɓun bāyinka, ka wanke rūhun māsu ƙaunar ka, in sāmu īkon mayar da fuskāta wajenka, kullum, kuma cikin kōwane hāli.
Kai nē Jalla sarkin sarauta, mayalwaci. Bābu wani Allah illā kai, mai shirya kōmi, maɗaukaki masani.
Idan kā zāɓi yin wannan salla, a bāyan kā yi arwalla, sai ka jā wannan āyā tsakānin tsakiyar rānā da fāɗuwarta, sau guda kōwace rānā.
Nā shaida yā Ubangijina, da kā halitto ni, don in san ka, kuma in yī maka sūjada. Nā tabbata a wannan lōkacin, kāsāwāta da iyāwarka, talaucīna da arzikinka.
Bābu wani Allah sai kai, mai cēto cikin matsala, mai rāyuwa cikin īkonsa.